Labarai
Putin Ya Yi Iƙirarin Lashe Zaɓen Rasha A Karo Na Biyar
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce nasararsa a zaɓen shugaban kasar ta nuna karara yarda da mutane ke da shi kan muradunsa.
A jawabin da ya gabatar bayan sakamakon zaɓe ya nuna ya samu kusan kashi 90 cikin100 na kuri’un da aka kada, Mista Putin ya ce idan ‘yan Rasha suka haɗa kansu babu wanda zai yi musu barazana ko dannesu.
Kusan a bayyana yake cewa Vladimir Putin zai yi ikirarin nasara a karo na biyar na wannan zaɓe da gagarumin rinjaye, duk da cewa ya fuskanci adawa daga ‘yan takara uku da ake yiwa kallon ‘yan koren gwamnatin Kiremlin.
Yayin da jami’an zaɓe suka sanar da cewa Putin ya samu sama da kashi 87 na kuri’un da aka kada, ya fito yana ikirari. cewa dimokuradiyar Rasha tafi ta kasashen yammanci sahihanci.
A tsokacinsa kan yaƙin Ukraine, ya ce abin da zai bai wa fifiko a yanzu shine sake karfafa sojojin Rasha. Ya kuma ce sojojinsa jajirtatu ne a fagen yaƙi da Ukraine.
Ya ce “Kullum sake nausawa muke yi. Sannu a hankali, cikin hikima, kuma a koda yaushe. Wannan ya zarta batun kare kai kaɗai. Salonmu ya sha bamban”.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
