Labaran Ketare
Mutuwar Navalny ta janyo zanga-zanga, alhini da kuma kame a duniya

Mutuwar jagoran adawar Rasha Alexei Navalny a gidan yari ta janyo ɓarkewar zanga-zanga da alhini a faɗin duniya.
Magoya bayan ɗan gwagwarmayar siyasar, sun taru a wajen ofisoshin jakadancin Rasha a ƙasashen waje da sauran wurare a faɗin duniya, ciki har da biranen Landan da Paris da Geneva da kuma New York.
A birnin Berlin na ƙasar Jamus dandazon mutane sun yi ta faɗin cewa ‘A kai Putin Kotun Duniya’, haka a a ofishin jakadancin Rasha da ke birnin Landan masu zanga-zangar sun riƙe kwalayen da ke nuna cewa ”Navalny ne gwarzonmu”.
Fiye da mutum 100 ne kuma suka tsaya a gaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva, inda suka riƙe hotunan Navalny tare da ajiye furanni.
Haka ma an gudanar da zanga-zanga a Rasha.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan sad zumunta sun nuna yadda mutane ke ajiye furanni a biranen Moscow da Saint Petersburg domin nuna alhininsu ga rasuwar jagoran adawar.
Rahotoni sun ce fiye da mutum 100 aka tsare sakamakon zanga-zangar a biranen Rasha.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari