Kasuwanci
Gwamnan Jigawa Namadi Na Jagorantar Ziyarar Nazarin Noman Alkama a Habasha

Gwamnan jihar Umar Namadi ya fara wani gagarumin ziyarar gani da ido zuwa kasar Habasha tare da wata babbar tawaga da ta hada da manyan mataimaka a harkokin noma, jami’ai, da kwararru daga ma’aikatar noma ta jihar da hukumomin da abin ya shafa.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya raba wa gidan rediyon Najeriya ya bayyana cewa, makasudin ziyarar shi ne nazarin shirin noman alkama na kasar Habasha da kuma gudanar da wani cikakken shiri da manufar dawowa gida sabbin dabaru da kwarewa zuwa gida
A cewarsa, alkama, kasancewarta ta biyu mafi girman abin bukata a duniya, tana da matukar muhimmanci wajen magance kalubalen samar da abinci a duniya.
Ya ce, a bisa wannan yanayin, Habasha ta zama babbar jigo a fannin noman alkama a Afirka, wanda ya nuna gagarumar nasarar da aka samu wajen dorewar noma da samar da albarkatu.
Hamisu Mohammed Gumel ya ci gaba da bayyana cewa, ziyarar na da manufar cimma muhimman manufofi da suka hada da tantance shirin noman alkama na kasar Habasha da kuma fa’idarsa.
Ya yi nuni da cewa, sauran muradun sun hada da samar da hanyoyin yin musanyar ilimi kan tsarin noman alkama, da magance kalubalen da ake fuskanta wajen samar da alkama mai dorewa, da inganta hadin gwiwa tsakanin Habasha da Najeriya wajen daukar sabbin dabarun noma.
Ya bayyana cewa musamman wuraren da aka fi mayar da hankali a kai sun hada da fahimtar tsare-tsare na dogon lokaci na Habasha na noman alkama, da tantance ci gaban da aka samu da kalubale, da binciko hanyoyin samar da kayayyaki daban-daban, da kuma baje kolin ingantattun samfura kamar noma kasuwanci.
Ya ce, a ziyarar aiki ta kwanaki hudu, tawagar ta Jigawa, da wasu muhimman abubuwa, za su dauki darussa kan noman ruwan sama da noman alkama na ban ruwa a jihohi daban-daban na kasar Habasha, da kuma samun nasarar samar da alkama mai dorewa.
Hakama yayi nuni da cewa, jihar Jigawa a halin yanzu ita ce kan gaba wajen noman alkama a Najeriya, wanda ke bayar da gudunmawa sosai a fannin noma da samar da abinci, kuma ana sa ran rangadin binciken zai bude wa jihar damammaki tare da cimma wasu muhimman sakamako da za su taimaka wajen bunkasa noman alkama mai dorewa a jihar.
Gumel ya kara da cewa, ziyarar ta jaddada kudirin gwamnatin Gwamna Umar Namadi a jihar na binciko sabbin hanyoyin noma domin inganta samar da abinci da kuma mayar da harkar noma sana’ar kasuwanci ga al’ummar jihar da galibin masu noma ne.
USMAN MZ?Wababe
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27