Ilimi
Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto Za Ta Yaye Dalibai Dubu 23

Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto ta ce za ta yaye dalibai dubu ashirin da biyu da dari tara da talatin da biyu wadanda suka yi nasarar kammala karatunsu a fannoni daban-daban a Jami’ar.
Shugaban jami’ar Farfesa Lawal Suleiman Bilbis ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da nufin fadakar da jama’a game da taron gangamin da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Afrilun 2024 kuma ake sa ran kammala shi a ranar ashirin ga wannan wata.
Ya bayyana cewa bikin shi ne karo na 38, 39, 40 da kuma 41 na Jami’ar.
Farfesa Bilbis ya bayyana cewa, za a gabatar da wata lacca da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Rabado zai gabatar kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar arewacin kasar, wanda aka shirya a ranar 18 ga watan Afrilu.
Shugaban jami’ar ya kara da cewa taron zai kuma bayar da lambar yabo ga wasu fitattun mahalarta taron.
NASIR MALALI/Wababe
-
Labarai3 days ago
Gwamna Uba Sani Ya Nada Sarkin Kauru Amirul Hajj Na Shekarar 2025
-
Labarai6 days ago
Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Ta Raba Abinci, Tufafi Ga Marayu, Mabukata Da Malamai
-
Labarai5 days ago
Gwamnatin Jigawa Ta Nanata Dokar Haramta Kiwon Dare
-
Labarai5 days ago
GMBNI Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Gillar Wani Almajiri A Jihar Jigawa
-
Ilimi6 days ago
Gwamna Yusuf Ya Yi Sabbin Nade-Nade A Kano
-
Ilimi6 days ago
Hajjin Bana: Maniyata 3, 155 Suka Yi Rijista a Kano
-
Labarai6 days ago
IAR da NAERLS Sun Shirya Taron Tattaunawa Da Masu Ruwa Da Tsaki Kan Noma Dawa A Najeriya
-
Ilimi4 days ago
An Aika Dan Canji Da Dan Walawala Gidan Yari A Kwara