Fasaha
Majalisar Dattawa Ta Nemi Ministan Ilimi Ya Gurfana Gabanta
Majalisar dattawa ta gayyaci ministan ilimi da hukumar bayar da tallafin karatu ta tarayya bisa jinkirin biyan dalibai hakkokinsu.
Majalisar dattawa a ranar Talata ta umurci kwamitinta kan ilimi da ya gayyaci hukumar bayar da tallafin karatu ta tarayya da kuma ministan ilimi don bayar da cikakken rahoto kan halin da daliban Najeriya ke ciki a shirye-shiryen bayar da tallafin karatu na kasa da kasa ciki har da rashin biyansu hakkokinsu.
Kudurin dai ya biyo bayan kudirin da Sanata Saliu Mustapha (APC Kwara ta tsakiya) ne ya dauki nauyi.
Sanata Mustapha a cikin kudirin ya yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa tare da warware kalubalen biyan kudin makaranta da sauran matsalolin jin dadin da daliban Najeriya ke fuskanta kan shirin gwamnatin tarayyar Najeriya da kasashen waje da na kasashe renon Ingila, inda ya koka da halin da wadanda suka ci gajiyar tallafin ke fuskanta.
Ya bayyana cewa, wasu rahotannin da ke nuna cewa daliban Najeriya na fuskantar wahalhalu a kasashen Aljeriya, China, Morocco, Rasha da kuma Birtaniya, sakamakon rashin biyan kudin karatu da alawus din rayuwa, lamarin da ke haifar da yada labaran karya da kuma kunyata kasa.
Don haka Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya takunkumin da ya dace a kan jami’an Hukumar bayar da tallafin karatu ta Tarayya da kuma Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya wadanda ke da alhakin wannan gazawar.
Ya kara da cewa rashin cika alkawurran da gwamnatin tarayya ta yi na kudi a karkashin wadannan yarjejeniyoyin duniya sama da watanni goma, zai kawo cikas ga walwala da ci gaban karatun daliban da abin ya shafa.
Bashir M/Wabbae
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
