Labarai
Gwamnan Kano Ya Bada Umurnin Kama Duk Wanda Ya Fito Zanga-Zanga A Jihar
Gwamna Yusuf ya haramta duk wata zanga-zanga a bainar jama’a, umarnin kama wasu dalibai da ake zargin sun yi zanga-zanga
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya takunkumi mai tsauri kan duk wani taron jama’a da aka yi niyyar gudanar da zanga-zanga a jihar, tare da yin amfani da ikon da aka bashi a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, kuma aka aikawa gidan rediyon Najeriya a Kano.
Sanarwar ta ce, bisa ga matsayinsa, gwamnan ya umarci ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, da hukumar tsaro ta Civil defense ta Najeriya da su kama, tsare, da gurfanar da duk wani mutum ko kungiyar da ke gudanar da zanga-zanga a kan titunan Kano. .
Wannan ƙwaƙƙwaran mataki dabara ce ta riga-kafi da nufin kawar da duk wata yuwuwar tabarbarewar doka da oda da maƙiyan jihar suka shirya.
“Muna samun sahihan bayanan sirri da ke nuni da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa a Kano sun tsara shirin daukar nauyin kungiyoyin dalibai da masu fafutukar siyasa daga wasu jihohin Arewa maso Yamma domin tada hargitsi a fake da cewa suna goyon bayan tsigaggen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero. .”
Gwamnatin jihar ta fito karara ta haramta zanga-zanga ko jerin gwano ko wace iri ce, kuma za a kama mutanen da aka samu a kan titunan Kano suna yin irin wadannan ayyuka nan take.
“Ta wannan sanarwar, muna gargadin kungiyoyin dalibai da su guji yin amfani da masu tayar da kayar baya wadanda suka jajirce wajen tada rikici a Kano.”
Gwamnan ya bukaci daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum domin jihar ta ci gaba da zaman lafiya, kuma gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin don gaggauta maganin duk wani mutum ko kungiyar da ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da jihar ke samu a halin yanzu.
Saki/Abdullahi Jalaluddeen/Kano/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
