Kasuwanci
‘Yan Sanda Zasu Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Bukukuwan Sallah A Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ba da tabbacin a shirye ta ke na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa kafin, lokacin da bayan bukukuwan Sallah karama da za a fara gobe laraba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammad Hussein Gumel ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya, malamai da sauran masu ruwa da tsaki da suka shafi tabbatar da tsaro.
Ya ce dukkan hukumomin tsaro za su kasance cikin shiri a kowane lungu da sako da niyyar tabbatar da gudanar da bukukuwan Sallah lamui lafiya.
CP Mohammad Hussein Gumel ya lura cewa rundunar ta riga ta tattara dukkan rahotannin sirrin tsaro da ake bukata, don haka akwai bukatar a aiwatar da tsarin da zai tabbatar da zaman lafiya.
Ya yi kira ga sarakunan gargajiya da malamai da su hada kai da jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa jihar Kano ta samu zaman lafiya sakamakon hadin kai da ke tsakanin jama’a da jami’an tsaro.
“Mun tsara dabarun inganta tsaro, kuma muna da kwarin gwiwar cewa shawarwarin za su yi aiki yadda ya kamata wajen ganin mun shaida bukukuwan Sallah lafiya kalau.”
A jawabansu daban daban wakilan sarakunan Bichi da Gaya Alhaji Nura Ahmed madakin Bichi da Alhaji Bashir Albasu, makaman Gaya sun yaba da kokarin da kuma jajircewar rundunar ‘yan sandan Kano na ci gaba da aiki babu kama hannun yaro wajen dakile ayyukan miyagun ayyuka a jihar.
“Wannan taron ya dace da lokacin da ya dace, saboda batun tsaro alhakin kowa ne, don haka akwai bukatar mu hada kai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a cewar wakilan sarakunan da suka halarci taron.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Labarai2 days ago
Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa
-
Labarai5 days ago
Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano
-
Fasaha3 days ago
An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar
-
Kasuwanci3 days ago
Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA
-
Ilimi6 days ago
Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno
-
Ilimi3 days ago
Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert
-
Labarai5 hours ago
An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa