Kasuwanci
Gobara Ta Lakume Kayayyaki Na Miliyoyin Naira A Kano
Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta lalata sama da shaguna 50 da kadarori da kudin su ya kai naira miliyan 150 a kasuwar ‘yan katako da ke Rijiyar Lemuo a karamar hukumar Fagge ta Kano.
Da yake zantawa da manema labarai shugaban kasuwar Alhaji Mamuda Musa Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe daya na daren Lahadi.
Ya yi nuni da cewa, gobarar ta kona sama da shaguna 50 da ke dauke da katako, da kumfa, da injin fkujeruda kujeru da sauran kayayyakin aiki.
Alhaji Mamuda ya ce har yanzu ba a kai ga gano musabbabin faruwar lamarin ba.
Shugaban kasuwar ya yabawa hukumar kashe gobara ta jihar Kano bisa gaggauta daukar matakan dakile gobarar.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafya’yan kasuwar da lamarin ya shafa.
Daga Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
