Labarai
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Dauki Matakan Kawar Da Nama Me Guba A Kasuwannin Jihar
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan kare lafiyar jama’a a daidai lokacin da ake ta yayata jita-jitar sayar da naman Sa me guba a wasu kasuwannin jihar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinar lafiya ta jihar, Dr. Amina Ahmed El-Imam ta fitar, ta ce an kafa wata babbar tawaga don sanya ido kan lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa, gwamnatin jihar ta kwace dukkan naman da ake zargi domin yin gwaji akan su, bayan wata ganawa da aka yi da masu ruwa da tsaki naKasuwar.
Sanarwar ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, yayin da ake ci gaba da bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.
Sanarwar ta kuma yabawa shugabannin kasuwar bisa hadin kan da suka bayar don shawo kan lamarin.
Sama da shanu talatin da uku 33 ake zargin sun mutu sakamakon guba a yankin Atere da ke Ilọrin.
An kuma yi zargin cewa an yanka matattun dabbobin ne aka raba wa mahauta domin sayarwa a kasuwanni.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
