Labarai
Liverpool Ta Koma Ta Biyu A Gasar Premier
Liverpool ta koma ta biyun teburin gasar Premier, bayan da ta ci Fulham 3-1 a Craven Cottage wasan mako na 34.
Liverpool ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Trent Alexander-Arnold a bugun tazara, daga baya Fulham ta farke ta hannun Timothy Castagne.
Daga baya ne Liverpool ta kara na biyu ta hannun Ryan Gravenberch, sannan Diogo Jota ya zura na uku a raga a Craven Cottage.
Kwallo ta 100 da Jota ya ci a babbar gasar tamaula ta Ingila a dukkan fafatawa, wanda ya zura 44 lokacin da yake Wolverhampton da kuma 56 a Liverpool.
Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta biyu da maki 74, iri daya da na Arsenal, wadda take kan teburi, sakamakon cin Wolves 2-0 ranar Asabar a Molinuex.
Manchester City, wadda ta kai wasan karshe a FA Cup ranar Asabar, bayan doke Chelsea tana ta ukun teburi da maki 73.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
