Labarai
Mutane 10 Sun Mutu A Hadarin Jiragen Soji A Malaysia
Mutane goma ne suka mutu a lokacin da wasu jirage masu saukar ungulu na sojojin Malaysia biyu suka yi karo da juna, yayin wani atisaye da suke yi a yau Talata.
Babban ami’in gudanarwa na hukumar kwana-kwana da aikin ceto ta kasar, Suhaimy Mohamad Suhail ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Firaministan kasar Anwar Ibhrahim ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasu a hadarin da ya bayyana a matsayin mai tada hankali, inda ya ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin faruwarsa.
Ba kasafai aka cika samun aukuwar hadarin jiagen sama masu saukar ungulu a kasasshen da ke shiyyar Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya ba, amma a watan da ya gabata, wani jirgin sama mai saukar ungulu na jami’an da ke tsaron gabar ruwan Malaysiyan yayi hadari a mashigar Malacca, duk da dai ba a samu asarar rai ba.
Haka nan a shekarar 2016, akwai mataimakin ministan kasar da ya rasu a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Sarawak da ke kasar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
