Labarai
Ƙungiyar Jigawa FADAMA CARES Ta Taya Shugaban Hukumar Sauya Fasalin Noma Ta Jihar Murna
Ƙungiyar Jigawa FADAMA CARES ta taya murna ga Dr. Saifullahi Umar bisa nadin sa a matsayin Daraktan Janar na farko na Hukumar Sauya Fasalin Noma ta Jihar Jigawa (JATA).
Nadin Dr. Saifullahi Umar ya samu amincewar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi a kwanakin baya.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na FADAMA CARES, Ibrahim Ibrahim ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana wannan naɗi a matsayin shaida ga jajircewa, ƙwarewa da gagarumar gudunmawar Dr. Umar a matsayinsa na mai ba da shawara kan harkokin noma ga Gwamna.
Sanarwar ta ƙara da nuna tabbacin cewa a ƙarƙashin jagorancinsa, JATA za ta jagoranci sauye-sauye masu ma’ana, ta ƙarfafa kirkire-kirkire, tare da sauya fannin noma a Jigawa bisa daidaito da shirin manufofi 12 na Gwamna Namadi.
Ƙungiyar Jigawa FADAMA CARES ta kuma yi addu’a ga Allah Ya kara hikima da nasara ga Dr. Saifullahi Umar domin sauke wannan nauyi da aka dora masa.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
