Labarai
Marasa Lafiya A Nasarawa Sun Koka Game Da Yajin Aikin Likitoci
Daga Aliyu Muraki
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin.
Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta biya dukkan hakkokinsu da ke karuwa zuwa biliyoyin naira.

A yayin ziyarar, ya ruwaito cewa nas nas da ungozoma ne kawai ke kula da marasa lafiya, musamman a sashen bada kulawar gaggawa, inda suke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da ake tura waɗanda lamuransu ke neman kulawar likitoci zuwa wasu asibitoci domin samun kulawar gaggawa.
Haka zalika su ma likitocin Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya (FMC) KKeffisun bi sahun takwarorinsu wajen shiga yajin aikin.
Hakan ya tilastawa marasa lafiya barin asibitocin domin komawa asibitoci masu zaman kansu a cikin biranen biyu, yayin da wasu kuma suka koma gida suna jiran tsammani.

A tattaunawa da wasu marasa lafiya, Gloria Namo da Jamil Ishaq, da ke jinya a asibitocin, sun bayyana damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya ta kasa biyan bukatun likitocin, wanda hakan ya hana su ci gaba da samun kulawa.
Sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan dukkan haƙƙin likitocin, ganin cewa ba za su iya zuwa asibitoci masu zaman kansu ba saboda tsadar rayuwa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
