Labarai
Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba Wa Karamar Hukumar Gusau Bisa Shirin Tallafawa Jama’a
Daga Aminu Dalhatu
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, bisa shirin tallafawa jama’a domin dogaro da kai da kuma inganta rayuwarsu.
Ta yi wannan yabo ne yayin bikin kaddamar da kayan tallafi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa, kayayyakin da aka raba sun haɗa da motoci, babura, injinan dinki, injinan niƙa, keken guragu, kayan abinci da kuma tallafin kuɗi a fadin ƙaramar hukumar.
Ta bayyana shirin a matsayin abin yabo da ke tallafawa iyalai, wanda ke karfafa dogaro da kai, tare da rage matsin tattalin arziki a tsakanin al’umma.


Uwargidan Gwamnan ta taya waɗanda suka amfana da shirin murna, tare da shawartarsu da su yi amfani da kayan yadda ya kamata domin inganta rayuwarsu da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma.
A wani bangare kuma, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta karɓi tawagar mata da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki.

Uwargidan Gwamnan ta tabbatar wa sabbin mambobin jam’iyyar da cewa za a ba su dama da haɗin kai a dukkan harkokin jam’iyya, tare da kira gare su da su ba da goyon baya ga hangen nesan gwamnatin wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki da dorewar cigaba a fadin jihar.
A nata jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, ya ce an shirya wannan tallafin ne domin taimakawa masu buƙata su dogaro da kansu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
