Kasuwanci
An Bukaci Mazauna Rukunin Gidaje Harmony Su Rika Biyan Bashin Gidajensu
An bukaci mazauna Rukunin gidajen Harmony da ke jihar Kwara da su ƙara ƙaimi wajen biyan bashin lamunin gidajensu (mortgage), domin bai wa wasu ma damar cin gajiyar shirin mallakar gidaje.
Manajan reshen Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria – FMBN) na jihar Kwara, Alhaji Nurudeen Aliyu Muhammed, ne ya yi wannan kira a yayin bikin rantsar da mambobin kwamitin mazauna Harmony Estate da aka gudanar a Ilorin.
Ya bayyana cewa yawancin mazauna gidan ba su cika ka’idojin mallakar gidajen ba saboda rashin cika sharuddan biyan bashin.
A cewarsa, bankin ya yi haƙuri tsawon lokaci tare da barin masu zama a gidajen ba tare da biyan kuɗaɗen da suka dace ba.
Alhaji Nurudeen ya gargadi mazauna da su yi abin da ya dace domin kauce wa korar su daga gidajen.
Ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba bankin zai fara gina wani sabon rukuni na gidaje da za a sayar da kowanne a kan kuɗi Naira miliyan 25.
Manajan ya ƙara da cewa za a samar da sabbin matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron lafiyar al’ummar yankin.
A nasa jawabin yayin bikin rantsar da kwamitin, Shugaban Mazauna Harmony Estate Ilorin, Malam Otepola Adeolu, ya shawarci mambobin kwamitin da su kasance masu halartar tarurrukansu cikin lokaci.
Ya ce manufar kafa kwamitin ita ce bai wa mambobin damar samun sahihin bayani kai tsaye kan al’amuran da suka shafi mazauna gidan.
Malam Adeolu ya kuma shawarci mazauna yankin da su tabbatar suna biyan kuɗaɗen wata-wata da na wutar lantarki da ruwa yadda ya kamata.
Haka zalika, ya bukaci mambobin kwamitin da su rika adana bayanan ayyuka da kuma cikakkun bayanai na dukkan mazauna gidaje kusan 500 da ke cikin estate ɗin.
Shugaban ya yi kira ga hadin kan dukkan mambobi domin tabbatar da nasarar aiwatar da ayyukansu a sabuwar shekara.
Ali Muhammad Rabiu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
