Labarai
Karamar Hukumar Birnin Kudu Za Ta Samar da Kekunan A-Daidaita-Sahu Don Zirga-zirgar Mata
Daga Usman Muhammad Zaria
An yi kira ga Gwamnatin Jihar Jigawa da ta dauki kwararan matakai don dakile dabi’ar sare bishiyoyi a fadin jihar.
Tsoho Gwamnan Jihar, Barrister Ali Sa’ad Birnin Kudu ya yi wannan kiran a lokacin taron muryar Birnin Kudu karo na 7 da aka gudanar a Birnin Kudu.

Barrister Ali Sa’ad Birnin Kudu
Ali Sa’ad Birnin Kudu wanda shi ne shugaban babban taron ya bukaci al’ummar garin Birnin Kudu da su mayar da hankali matuka ga al’amuran tsaro da ilimi da samarwa matasa ayyukan yi domin janye su daga tu’ammali da miyagun kwayoyi da sace sace.

Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban riko na Muryar Birnin Kudu, Alhaji Ahmad Sa’id Kangire, ya ce kungiyar ta jagoranci bincike akan harkokin lafiya da ilimi tare da ci gaba da fafutukar kafa kwalejin ilimi ta musamman ta tarayya da kokarin kafa kananan ofisoshin ‘yan sanda a sassan garin Birnin Kudu.

Farfesa Muhammad Abubakar Birnin Kudu
Kangire, ya ce kungiyar ta kuma yi kokarin nemo mafita ga karancin ruwan sha da koyar da matasa sana’o’i domin kauwar da su daga miyagun dabi’u zuwa turbar dogaro da kai.
A jawabinsa, sakataren Gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim, ya bayyana taron a matsayin alamar da ke nuni da cewar Muryar Birnin Kudu ta samu karbuwa a wurin jama’a.

A don haka, ya ja hankalin daidaikun mutane su kasance masu bada gudummawa da mafi kankantar abin da suka mallaka da kuma karfinsu da shawara ta gari don cimma burin da aka sanya a gaba.

A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Dr Builder Muhammad Uba, ya bada tabbacin samar da Keken A-Daidaita-Sahu domin zirga zirgar mata a cikin gari kamar yadda daya daga cikin mata da suka halarci taron ta mika koke.

Dangane da matsalar sare bishiyoyi barkatai kuwa, Dr. Builder Muhammad Uba ya ce karamar hukumar za ta dasa bishiyoyi milyan 2 domin amsa umarnin Gwamna Umari Namadi na daukar irin wannan mataki.
Cikin wadanda suka halarci taron, sun hada da Babban Malamin addinin musulunci, Farfesa Abubakar Sani Birnin Kudu da Abdullahi Garba Birnin kudu da masu rike da sarautu, da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
