Connect with us

Labarai

Majalisar Dattijai Ta Bukaci Karfafa Jarin Bankin Lamunin Gidaje Na Tarayya

Published

on

Majalisar dattawan na shirin yin amfani da bangaren zartaswa na gwamnati kan gaggauta samarda kwakkwaran jari ga babban bankin bayar da lamunin gidaje na gwamnatin tarayya (FMBN) domin bunkasa karfinsa na samar da gidaje masu saukin kudi ga ‘yan Najeriya da kuma magance matsalar gibin gidaje a kasar nan.

Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da gidaje da raya birane, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin hukunar gudanarwar bankin yayin zaman kasafin kudin shekarar 2025 a harabar majalisar dokokin tarayya da ke Abuja.

Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya yaba da yadda Bankin yake aiwatar da kasafin kudin shekarar 2024, ya nuna damuwarsa kan yadda ake kasafta kasafin kudin shekarar 2025, duba da irin rawar da bankin ke takawa wajen magance bukatun gidaje na miliyoyin ‘yan Najeriya.

Shugaban kwamatin, ya shawarci mahukuntan Bankin bada jinginar gidaje da kada su karaya da dan karamin kason da ake yi musu, inda ya ba su tabbacin cewa shugabannin majalisun biyu za su shiga tsakani domin magance kalubalen da ke kawo cikas ga ayyukan bankin.

Manajin Darakta na Babban Bankin Lamuni na Tarayya, Alhaji Shehu Usman Osidi, tare da tawagar sa yayin kare kasafin kudin 2025 a Zauren Majalisar Tarayya, Abuja.

Tun da farko, Manajan Darakta na Bankin bada jinginar gidaje na Najeriya Alhaji Shehu Usman Osidi, ya ce bankin ya bullo da jerin rancen da za a samu ga masu karamin karfi amma rashin jari ya zama babban cikas da ya hana aiwatar da su.

Alhaji Shehu Usman Osidi, wanda ya yaba da jajircewar da majalisun biyu suka yi na mara musu baya, ya kuma tabbatar da cewa bankin ya jajirce wajen ganin an aiwatar da sabon ajandar fatan da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa hannu, ta hanyar samar da gidaje ga jama’ar Najeriya.

A tasa gudunmuwar, babban daraktan lamuni Dr Muhammad Sani Abdullahi, ya bayar da shawarar a sake duba wasu dokoki da suka kafa ayyukan bankin duba da irin dimbin koma baya da suke haifarwa ga ci gaban bankin.

Dakta Sani Abdullahi, ya tabbatar da cewa a halin yanzu bankin yana aiwatar da ayyuka da dama a jihohin Bayelsa, Osun, Sokoto, Bauchi, Kebbi, da Zamfara duk da karancin jarin da ke da shi yayin da miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na kasar ke neman lamuni don gyara gidajensu.

Babban daraktan ya kuma yi fatan cewa idan har majalisar ta goma ta shafi batutuwan da bankin jinginar gidaje ya tabo yayin kare kasafin kudin za a magance su yadda ya kamata domin ci gaban kasa.

COV/TSIBIRI

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara