Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Kano Ta Dawo Da Ayyukan Ma’aikatar Yada Labarai

Published

on

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya sanar da maido da kashi 85% na ayyukan da aka kwace daga ma’aikatar yada labarai.

 

Wannan yunkuri na da nufin farfado da ma’aikatar tare da inganta ayyukanta a jihar.

 

A cewar Waiya, maido da ayyuka wani muhimmin mataki ne na karfafa ma’aikatar da inganta ayyukanta.

 

Ya kara da cewa tuni ma’aikatar ta fara bullo da dabarun zamani domin bunkasa yada labarai a jihar Kano.

 

Wasu daga cikin tsare-tsaren da Waiya ta sanar sun hada da kafa dandalin ‘yan kasa na Kano, wanda zai samar da hanyar da ‘yan kasa za su ba da tasu gudummawar ci gaban jihar.

 

“Ma’aikatar za ta kuma shirya taron mu’amala a kowane wata uku tsakanin gwamnati da ‘yan kasa don magance matsalolinsu da burinsu”

 

 

Kwamishinan ya bayyana cewa, ma’aikatar za ta hada gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu (CBOs) a fadin kananan hukumomi 44 domin zama jakadun shugabanci na gari.

 

“CBOs za su yi aiki don tabbatar da cewa ‘yan ƙasa sun ci moriyar dimokuradiyya ta hanyar ayyukan ci gaba”

 

Waiya ya kuma bayyana abubuwan da gwamnatin jihar ta sa a gaba, da suka hada da bunkasa tattalin arziki, ilimi, da kuma maido da yara kanana.

 

Ya yi nuni da cewa gwamnati ta baiwa tattalin arziki fifiko ta hanyar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin gyara masana’antu tare da neman hadin gwiwa a bangaren wutar lantarki.

 

“Gwamnatin ta kuma kafa dokar ta-baci a fannin ilimi, inda ta samar da tufafin makaranta da littattafai kyauta ga dalibai”

 

“Bugu da kari kuma, gwamnatin jihar ta kafa wani babban kwamiti domin tabbatar da an dawo da yaran kan tituna gida”.

 

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, maido da ayyukan ma’aikatar yada labarai ana sa ran zai karawa gwamnatin jihar damar tattaunawa da ‘yan kasar yadda ya kamata tare da magance matsalolinsu.

 

KHADIJAH ALIYU/Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara