Labarai
Hukumar Shige da Fice Ta Gargadi Jama’a Kan Sabuwar Kungiya Achad Life Mission
Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta bayyana damuwa kan bullar wata sabuwar kungiya mai suna Achad Life Mission International.
A wata sanarwa da Babban Jami’in Ma’aikatan na ofishin Kwamptroller Janar na Hukumar, AA Aridegbe, ya fitar, an gargadi jama’a da su kasance masu lura tare da bayar da rahoton duk wasu ayyukan da ke da alaka da kungiyar.
Sanarwar ta nuna cewa rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyar tana da hedkwata a Kaduna, kuma shugaban ta, Mr. Yokana, yana zaune a Jos, Jihar Filato, an kuma ce kungiyar tana kira da a farfado da al’adun gargajiya na Afirka tare da watsi da addinin Musulunci da Kiristanci.
Bisa bayanan sirri, kungiyar tana daukar mambobi daga ciki da wajen Najeriya, kuma ana zargin tana da hannu a harkokin da suka saba doka kamar safarar mutane da raba yara da iyayensu, lamarin da ya sa ake bayyana damuwa game da barazanar da kungiyar ka iya kawowa al’umma.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumomi sun bayar da umarnin daukar mataki nan take, ciki har da kama duk wanda aka samu yana da alaka da kungiyar, domin rage barazanar da ayyukanta ka iya jawowa.
Hukumar Shige da Fice ta jaddada mahimmancin hadin kan jama’a tare da bin wannan umarni domin magance matsalar.
REL/UMAR S. FADA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
