Ilimi
Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Inganta Lafiya A Jihar Sakkwato
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta fannin kiwon lafiya a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idris Mohamed Gobir ya bayyana cewa yayin da ya karbi bakuncin sabuwar wakiliyar Unicef ta kasa Mrs Wafaa Sa’eed da ta kai ziyarar fahimtar da jihar.
Alhaji Idris Gobir ya ce a kan haka ne bangaren ke samun mafi yawan kasafin kudi tun hawan gwamnatin mai ci.
A wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai (Mataimakin Gwamnan) Garba Muhammed ya raba wa manema labarai, Mataimakin Gwamnan ya ce manufar ita ce a tabbatar da cewa mutane suna samun ayyukan kiwon lafiya cikin sauki.
Ya kuma nuna jin dadinsa da tallafin daban-daban da gwamnatin jihar ke samu daga Unicef domin inganta fannin lafiya.
Alhaji Idris Gobir ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bayar da duk wani goyon bayan da Unicef ke bukata domin gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali a jihar.
Tun da farko, sabuwar wakiliyar kasar Misis Wafaa Sa’eed ta ce ayyukan Unicef sun shafi jin dadin mutane musamman yara a duniya.
Misis Wafaa Sa’eed ta sanar da cewa Unicef za ta taimaka wa yara marasa galihu 18,000 a shirin inshorar lafiya a jihar.
Ta ci gaba da cewa Asusun ya samar da wayoyin hannu guda 200 da kuma abin caji wato Power Bank da kuma Kwamfutar laptop 3 na rijistar zamantakewa a jihar.
Wakilin Unicef na kasa tare da rakiyar sabon mataimakin wakilin kasar mai kula da ayyuka Mista Charles Opikoli Lolika ya bayyana jin dadinsa tare da hadin gwiwar da asusun ke samu daga gwamnatin jihar tare da fatan za a dore.
REL/MUSTAPHA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
