Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu
Daga Usman Muhammad
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu na shekarar 2026 a mazabu 30 da ke da wakilci a Majalisar Dokokin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
Ya ce ayyukan da aka amince da su sun haɗa da ginawa, kammalawa da gyaran masallatan Juma’a da na Kamsa Salawat, da kuma ginawa da gyaran gidajen hakimai da dagatai.
Sauran ayyukan sun haɗa da shimfiɗa tubalan kankare a wasu wurare da gina katangar da za ta kewaye makabartu.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ayyukan sun haɗa da girka na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, sayen janareto, samar da darduma a masallatai, da kuma tabarmi ga wuraren da aka ware.
A cewarsa, an tsara ayyukan ne domin biyan buƙatun da aka gano a kowace mazaba, tare da inganta wuraren da cibiyoyin addini, da na gargajiya da na al’umma ke amfani da su.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce waɗannan ayyuka za su taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samun wutar lantarki ta wasu hanyoyi, inganta wuraren da jama’a ke amfani da su da kuma bunƙasa jin daɗin al’ummomin da za su amfana da ayyukan.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
