Connect with us

Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Published

on

Daga AMINU DALHATU

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a baya-bayan nan, tare da tabbatar wa mazauna jihar cewa tana ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Mohammed Dantawasa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai kan halin tsaro na baya-bayan nan da aka gudanar a Gidan Gwamnatin jihar da ke Gusau, inda ya yi bayani kan matakan da gwamnati ke ɗauka domin yaƙi da ayyukan ’yan bindiga da kuma ƙarfafa kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Dantawasa ya ce an shirya taron ne domin amsa tambayoyin al’umma kan hare-haren, bayar da bayanai kan matakan tsaron da ake ci gaba da aiwatarwa, tare da sake jaddada aniyar gwamnati na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar jihar.

Ya bayyana cewa garuruwan Bindin da Falale da ke Ƙaramar Hukumar Maru, Damba da Wanke a Ƙaramar Hukumar Gusau, Bagega a Ƙaramar Hukumar Anka, da Moriki a Ƙaramar Hukumar Zurmi na daga cikin al’ummomin da hare-haren baya-bayan nan suka shafa.

Kwamishinan ya lura cewa hare-haren sun ƙara jefa mazauna yankunan cikin fargaba, tare da kawo cikas ga muhimman harkokin tattalin arziki da zamantakewa, ciki har da noma, kasuwanci da sufuri.

Mahmud Dantawasa ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa al’umma da fararen hula, yana mai bayyana irin waɗannan ayyukan laifuka a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, kuma barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar.

Ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati tana aiki tare da hukumomin tsaro da abin ya shafa domin ƙarfafa matakan mayar da martani ga sabbin barazanar tsaro da inganta kariyar al’ummomin da suka fi fuskantar haɗari.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara