Ilimi
An Gudanar da Liyafar Taya Murna ga Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Dutse
Daga Usman Muhammad Zaria
Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman Gumel, ya bayyana sabon Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Farfesa Ahmad Muhammed Gumel, a matsayin mutum mai son kawo cigaba ga al’ummarsa.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin liyafar karramawa da abokan Farfesa Gumel suka shirya masa a dakin taro na masarautar Gumel.
A cewarsa, bai yi mamakin yadda jama’a suka halarci bikin rantsar da Shugaban Jami’ar a Dutse da kuma liyafar da aka yi masa a Gumel ba, domin sabon Shugaban Jami’ar mutum ne mai kula da jama’a, abokan aikinsa da duk wanda ya taɓa hulɗa da shi.
Ya kuma bayyana cewa a lokacin da Farfesa Gumel yake ƙasar Malaysia, ya taimaka wajen samar wa da dama daga cikin mutanensa guraben karatu da tallafin karatu.
Ya buƙaci sabon Shugaban Jami’ar da ya kasance mai aiki bisa gaskiya, tare da yin adalci ga kowa, yana mai cewa yana da yaƙinin zai yi nasara a Jami’ar Tarayya da ke Dutse.
Dr. Najib Abdulhamid, wanda ke aiki da Microsoft Office a ƙasar Kenya, ya yi magana a madadin abokan sabon Shugaban Jami’ar, inda ya ce suna farin cikin ganin abokinsu tun daga yarinta ya kai kololuwar matsayinsa na aiki, kuma za su tallafa masa da addu’o’i da shawarwari domin ya zamto abin tunawa a tarihin jami’ar.
Ya ce sun yi nazari sosai kan tsare-tsarensa guda goma sha ɗaya, kuma suna da yaƙinin cewa zai mayar da hankali, jajircewa da kuma samun ƙwararrun ma’aikata, domin cimma manufofinsa, ya ce za kuma su yi amfani da alaƙarsu wajen taimaka masa ya cimma burinsa ga jami’ar.

A nasa jawabin, Farfesa Muhammed Sani Gumel, tsohon Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da harkokin karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya taya sabon Shugaban Jami’ar murna tare da ba shi shawarar fahimtar dokokin jami’a sosai.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
