Labarai
Durumbun Gusau Ya Bukaci Haɗin Gwiwa Wajen Magance Matsalar Tsaro
Daga Aminu Dalhatu, Gusau
Sabon Durumbun Gusau, Farfesa Aminu Ibrahim Gusau, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Zamfara, tare da inganta tattara bayanan sirri da ƙara shigar al’umma cikin ƙoƙarin magance matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar jihar.
Ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, bayan mai martaba Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, ya naɗa masa sarautar gargajiya ta Durumbun Gusau. Ya kuma bayyana godiyarsa bisa wannan karamci.
Farfesa Gusau ya ce magance matsalar tsaro na buƙatar cikakken tsari da zai haɗa hukumomin tsaro da cibiyoyin gwamnati da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya lura cewa Gwamna Dauda Lawal ya nuna jajircewa tare da yin ƙoƙari wajen magance matsalar tsaron, sai dai ya ce ikon kundin tsarin mulki kan sojoji da ’yan sanda ya fi karkata ga Gwamnatin Tarayya.
A cewarsa, akwai buƙatar gwamnatocin biyu su samar da tsarin haɗin gwiwa da zai ba su damar tantance matsalolin tsaro tare, tsara hanyoyin magance su da kuma tura ƙwararrun ma’aikata masu gogewa domin shawo kan lamarin.
Ya bayyana kyakkyawan fata cewa idan aka samu haɗin kai na gaskiya, ingantattun bayanan sirri, shugabanci nagari da jajircewar kowa, Jihar Zamfara da Nijeriya baki ɗaya za su iya shawo kan matsalolin tsaro da suke fuskanta.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
