Labarai
‘Yan Kwana-Kwana A Kano Sun Ceto Rayukan Mutane 8 A Watan Mayu
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce mutane 8 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar bala’o’i daban-daban a cikin watan Mayun 2024.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
A cewarsa, hukumar kashe gobara ta jiha karkashin jagorancin Alhaji Hassan Muhammad ta ceci rayuka 10 da dukiyoyi na sama da naira miliyan 8.
Jami’in hulda da jama’a ya bayyana cewa kiyasin kadarorin da aka yi asarar sun kai nai 31,650, 700 a cikin watan da ake magana.
Saminu ya yi nuni da cewa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta samu kiraye-kirayen kashe gobara guda 51, kirar ceto 13 da kuma kararrawar karya 6 a dukkan gidajen kashe gobara 29 da ke jihar.
Ya ce an samu raguwar yawan tashin gobara yayin da jihar ta samu rahoton afkuwar gobara guda 222 a sassan jihar tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2024.
Jami’in hulda da jama’a ya lura cewa al’amuran da aka nada sun shafi gidajen zama, shaguna da gidajen mai.
Ya bukaci jama’a da su kiyaye tsaro a kowane lokaci tare da kai rahoton duk wani bala’i ga ofishin hukumar kashe gobara mafi kusa ko ta layukan wayar sa hukumar.
“Zan yi amfani da wannan damar wajen jawo hankalin jama’a da su kula da gobarar a hankali don gujewa afkuwar gobara.”
“Duk mai ababen hawa su rika tuki cikin kulawa tare da bin dokar hanya domin gujewa hadurran mota”.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
