Kasuwanci
Ina Son Lissafin Sabon Albashi Cikin Awa 48 —Tinubu
Shugaba Kasa Bola Tinubu ya umurci Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun, da ya lissafo abin da za a kasha idan Gwamnati ta biya sabon mafi karancin albashi na kasa.
Shugaban ya bayar da umarnin ne a Abuja lokacin da ya gana da mambobin kwamitin gwamnatin tarayya, inda suka yi masa bayanin sakamakon ta tattaunawa da akayi da kungiyar kwadago.
Bayan taron, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya ce an baiwa ministar kudi zuwa yau Laraba, domin ya ba da alkaluman da za su jkarawa gwamnati haske kan lamarin.
Ya bayyana cewa taron wanda ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu, karamin minista a ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Nkeiruka Onyejeocha, da kuma manajan darakta na Hukumar NNPC, Alhaji Mele Kyari, ya yi niyyar nemo daidaito tsakanin bayanin gwamnati da kuma idan aka aiwatar da shi tare da yanayin tattalin arzikin kasa.
Ministan ya jaddada cewa shugaban kasar ya kuduri aniyar samar da sabon mafi karancin albashi mai dorewa ga ‘yan Najeriya, wanda ya shafi ba gwamnatin tarayya kadai ba, har da jihohi da bangaren masu zaman kansu.
Ya ce gwamnati ba ta adawa da karin albashi, amma tana son tabbatar da cewa duk wata yarjejeniya da aka cimma ta dore kuma ta tabbata, idan aka yi la’akari da yanayin tattalin arziki a kasa.
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
