Kasuwanci
Gwamnatin Taraba Ta Shirya Rarraba Taraktoci Noma
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas amince da tsarin kwamitin rabon tarakta a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Cif Timothy Kataps ya sanyawa hannu, kuma babban sakataren yada labaran gwamnan, Yusuf Sanda ya bayyanawa manema labarai.
Sanarwar ta ce kwamishinan noma da samar da abinci na jihar, Farfesa Nickolas Nemesson ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba.
Mambobin sun hada da shugaban RIFAN na jiha, Tanko Bobbo Andami, wakilan kungiyar kwadago, Mr. Gara Nuga daga kungiyar matasa ta kasa (NYCN), da majalisar mata ta kasa (NCWS).
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Uchena Eschareturi, da Dr. Aminu Jauro Hassan, shugaban karamar hukumar Jalingo, mai wakiltar ALGON.
Sai dai Mista Samson Alhassan na ofishin sakataren gwamnatin jihar Taraba zai kasance sakataren kwamitin.
Sai dai har yanzu ba a bayyana ranar da za a fara rabon kayayyakin ba.
Sani Sulaiman/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
