Labarai
Gwamna Kefas Na Taraba Ya Karbi Katin Jam’iyyar APC
Daga Jamila Abba
Gwamnan Jihar Taraba, Dakta Agbu Kefas, ya karɓi katin shaidar zama dan jam’iyyar APC a hukumance, wanda hakan ya tabbatar da cikakken rajistarsa cikin jam’iyyar.
An mika katin membobinsa na APC ga Gwamnan ne ta hannun Shugaban APC a gundumar Asibiti (Hospital Ward) da ke Karamar Hukumar Wukari, Honarabul Umaru Tanko ne ya mika katin zama mamban na APC ga Gwamna Kefas a gidan TY Danjuma da ke Jalingo.
Da yake jawabi a ofishinsa bayan karɓar katin, Gwamna Kefas ya bayyana cewa rajistarsa ta tabbatar da matsayinsa a hukumance a matsayin cikakken mamba na APC, wanda hakan zai ba shi damar shiga dukkan harkokin jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a yi bikin sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar ta APC.
A yayin mika katin, Honarabul Umaru Tanko ya bayyana Gwamnan a matsayin cikakken mamba na APC tare da nuna farin cikin jam’iyyar na maraba da shi a hukumance.
Haka kuma, Kwamishinar yada Labarai da Wayar da Kai ta Jihar, Barista Zainab Usman Jalingo, ta tabbatar da cewa yanzu Gwamna Kefas cikakken mamba ne na APC a Jihar Taraba.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
