Kasuwanci
NSCDC Ta Kama Mutane 5 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Kano
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da sace wayoyin turakun lantarki dake kan hanyar motar unguwar Fagge zuwa Kofar Wambai.
Kwamandan Rundunar Falala ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.
Ya ce jami’an NSCDC na jihar Kano sun kama Adnan Umar mai shekaru 26 da Musa Shuayb 24 a wani sintiri da tsakar dare a kan hanyar IBB a Kano.
” Ana zargin su da lalata wayar wuta a kan titin IBB hanyar sabuwar kasuwar Fagge/Kofar Wambai, yayin da kuma suka yi yunkurin yin awon gaba da sundukai 3 nade da wayar kafin ma’aikatan hukumar dake sintirin dare su kama su.”
A wani labarin kuma, an kama wasu mutane 3 da ake zargin barayin babur ne ciki har da barawon zaune.
“An kama wadanda ake zargin Saminu Magaji a.k.a Pina mai shekaru 19, Haruna Idris mai shekaru 22 da kuma Ahmed Abubakar ( receiver) mai shekaru 38.”
Kwamandan ya kara da cewa, rundunar ta kama wasu mutane 2 da ake zargi da hannu a dumu-dumu.
“Wadanda ake zargin sun fito ne daga Gwammaja, karamar hukumar Dala, jihar Kano, kuma sun kware wajen fasa gidaje da satar babura da kayayyakin mutane.
Ya kara da cewa mutanen biyar din suna kan bincike kuma idan sun kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
