Labarai
INEC Ta Fuskanci Suka Kan Zaben Kauran Namoda
Jam’iyyun siyasa a Jihar Zamfara sun nuna mabanbantan ra’ayoyi kan zaben cike gurbi da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis, 21 ga watan Agustan 2025 a karamar hukumar Kauran Namoda.
A taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gusau, Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC a jihar, Dakta Mahmud Isah, ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye da ake bukata domin gudanar da zaben a rumfunan zabe da ke Kambarawa da Sakajiki.

Dakta Mahmud ya bayyana cewa an tura jami’an hukumar tare da na’urorin zamani. Ya kara da cewa hukumar za ta gudanar da sahihin zabe mai inganci da gaskiya.
Ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa an ba su cin hanci, yana mai bayyana wannan zargi a matsayin karya da kazafi.
A nasa jawabin, sakataren jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Nasiru Ibrahim, ya soki matakin INEC na gudanar da zabe a rumfunan zabe guda biyar kacal, maimakon goma sha daya.

Ya ce akwai bukatar a sake gudanar da zabe a rumfunan zabe guda shida da aka cire saboda kuri’u sun wuce na masu kada kuri’a. Ya ce rumfunan da aka cire suna da kuri’u sama da dubu hudu, don haka a gudanar da zabe a dukkan rumfunan goma sha daya domin adalci.
Ita kuwa jam’iyyar APC a Zamfara ta bakin sakataren yada labaranta, Yusuf Idris Gusau, ta bayyana shirinta na shiga zaben tare da nuna kwarin gwiwar nasara. Ya ce sanar da zaben a matsayin wanda bai kammalu ba ya yi daidai da dokar zabe, inda ya bukaci jam’iyyun da suka yi korafi su nemi hakkinsu ta kotun sauraren kararrakin zabe.
Haka zalika, shugaban jam’iyyar ADC a jihar, Kabiru Garba, ya ce jam’iyyarsa za ta shiga domin a fafata da ita, sai dai ya nuna damuwa kan yadda taron ya fi karkata ga jam’iyya guda.

A nasa bangaren, kwamishinan ’yan sandan jihar Zamfara, ta bakin mataimakin kwamishina mai kula da ayyukan ’yan sanda, Usman Dunguza, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa za a samar da tsaro mai kyau kafin, lokacin da kuma bayan zaben cike gurbin, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Taron ya tattaro wakilan jam’iyyu daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
