Kasuwanci
Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bunkasa Tattalin Arziki Na Farat Daya

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da shirin da ke da nufin ciyar da tattalin arzikin kasa zuwa wani sabon matsayi.
Da yake jawabi a wurin taron, shugaban ya ce shirin ba wai kawai wata manufa ba ce, a’a, magana ce mai kakkausar murya da ke nuna aniyar gwamnati na ci gaba, da wadata, da kuma jin dadin kowane dan Najeriya.
Ya ce a ko da yaushe ya yi imani da irin dimbin karfin da Najeriya ke da shi, yana mai cewa ‘yan kasar mutane ne da Allah ya albarkace su da juriya, da kirkire-kirkire, da kuma ruhin kasuwanci mara ja baya.
Sai dai shugaban ya nuna rashin jin dadinsa ganin cewa an dade ana taimakon ci gaban tattalin arziki sakamakon sarkakiyar da ke tattare da tsarin kasuwanci na kasar.
BELLO WAKILI/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
