Fasaha
Shugaba Tinubu Ya Haramta Fitar Da Man Kade daga Nijeriya
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya bayar da umarnin dakatar da fitar da ɗanyen man kaɗe daga ƙasar na tsawon watanni shida domin ƙarfafa sarrafa shi a cikin gida da bunƙasa harkar masana’antar man kaɗen wanda kashi 95 na masu sarrafawa mata ne.
Tinubu ya bayyana kaɗe a matsayin ‘arziƙin Najeriya da ke cikin daji’.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya sanar da matakin a wurin taron masu ruwa da tsaki daga ɓangarori daban-daban a Abuja’ kuma shi ne zai jagoranci kwamiti na musamman da aka kafa domin faɗaɗa shirin sarrafa kaɗe cikin gaggawa
Kashim ya ce wannan ba mataki ne na kawo cikas ga harkokin cinikayya ba, sai dai an ɗauki matakin ne domin samar da daraja ga ƙasar da ƙara samar da ayyukan yi da kuma ƙara kuɗaɗen shiga.
Najeriya na daga cikin ƙasashe mafiya samar da kaɗe a duniya, musamman a jihohin Neja da Kwara da Oyo inda take samar da kusan kashi 40 na ɗanyen man kaɗe a duniya, amma tana da kashi ɗaya ne kacal a kasuwar da darajarta ta kai dala biliyan 6.5.
Gwamnati ta kuma ce ana fitar da kusan tan 90,000 na kaɗe ba bisa ƙa’ida ba a kowace shekara, abin da ke sa masana’antun cikin gida gaza yin aiki yadda ya kamata.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa “Matakin zai iya samar da dala miliyan 300 duk shekara a nan gaba kaɗan tare da nufin nunka hakan nan da shekara ta 2027.
Bello Wakili, Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
