Labarai
Sojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
Sojojin Najeriya sun karɓi motocin Vanquisher Light Armoured Personnel Carriers da aka kera a cikin ƙasa daga kamfanin sarrafa makamai na kasa (DICON).
A yayin bikin karɓar motocin, Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa, Lafnal Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa wannan mika kayan aiki shaidar ikon Najeriya ne a fannin kera kayan soja.
Wakilinsa, na Hedkwatar Sojojin Ƙasa, Major General Bamidele Alabi, ya ce motocin za su ƙara inganta aikin sojoji a fannoni daban-daban na ayyukan soja.
Ya bayyana cewa wasu motocin da aka samar a baya sun nuna amincinsu yayin gwaje-gwajen aiki, wanda ya sa aka ba da umarnin kera ƙarin motocin don amfani nan take a fagen aiki.
A jawabin maraba, Daraktan Janar na DICON, Major General Babatunde Alaya, ya ce wannan mika kayan aiki mataki ne mai muhimmanci wajen samun dogaro da kai a fannin tsaro.
Ya jaddada cewa motocin an tsara su ne domin dacewa da yanayin aiki na Najeriya, kuma an kera su don ayyuka da dama.
Usman Sani
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
