Labarai
Uwargidan Gwamnan Jihar Kabi Ta Yaba Da Shirin Agajin Tukur Wasoso
Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasare-Nasir, ta yi kira ga mutane masu arziki da su dauki darasi daga aikin agaji na Alhaji Tukur Wasoso, saboda yadda yake tallafa wa al’ummar jihar musamman masu bukata ta musamman.
Nasare ta yi wannan kiran ne a Jega, ta hanyar wata sanarwa da Sakatariyar Manema Labaranta, Khadija Sa’idu, ta raba kyaututtuka da tufafi na Sallah ga marasa galihu.
Wacce ta wakilce ta wato Babban Sakatariyar Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Hajiya Aishatu Muhammad Maikurata, ta yi kira ga mutane masu arziki da su yi koyi da irin wannan kyauta, tana jaddada tasirin sa ga jin dadin al’umma da marasa galihu.
A jawabin sa, Alhaji Tukur Wasoso ya bayyana cewa wannan shekara ce ta 21 da yake gudanar da irin wannan aikin a kowanne Ramadan ga marasa galihu. Baya ga bayar da tufafin Sallah kyauta, ya kuma gina asibitin agaji a Jega domin bayar da kyaututtukan lafiya ga mata da yara a yankin.
Wasoso ya kuma kafa cibiyar koyon sana’o’i a garin Aliero domin koyar da mata da matasa kyauta, tare da bayar da kayan fara aiki domin su zama masu dogaro da kai.
Ya kuma gode wa uwargidan Gwamna saboda tallafinta ga gidauniyar a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma ba da naira miliyan biyar ga gidauniyar, inda ya bayyana cewa kimanin mutane 10,000 za su karɓi tufafin kayan Sallah kyauta a fadin jihar.
A jawabin su, Sarkin Kabi na Jega, Alhaji Arzika Bawa Jega, da Mai Kula da NASARA Foundation, Alhaji Abdurasheed Bala, duk sun yaba da aikin agajin na Wasoso, tare da kira ga mutane da su yi koyi da shi.
REL SANI DUTSINMA
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
