Labarai
FUGUS Za Ta Kafa Cibiyar Tarihi da Al’adu ta Zamfara
Shugaban Jami’ar Tarayya dake Gusau (FUGUS), Farfesa Tukur Adamu, ya bayyana shirin kafa Cibiyar Bincike da Rubuce-Rubuce kan Tarihi da Al’adu na Zamfara.
Farfesa Adamu ya yi wannan bayani ne yayin da yake jagorantar Majalisar gudanarwa ta jami’ar a ziyara ta girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad.
Sanarwa daga Babban Sakataren Bayani da Harkokin Jama’a na Jami’ar, Jamilu Ibrahim Gusau, ta bayyana cewa ziyara ta kasance wani bangare ne na huldar da Farfesa Adamu ke yi da masu ruwa da tsaki, yayin da yake tsara manufar gudanarwar sa.
Shugaban jami’ar ya tabbatar cewa gudanarwar sa za ta yi aiki kafada da kafada da Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, domin tabbatar da cewa al’ummar jihar za su amfana daga damar ilimi da ci gaban da FUGUS ke bayarwa.
A jawabin sa, Emir na Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, ya yaba wa Shugaban jami’a da ƙungiyar gudanarwa, ya bayyana ziyara a matsayin farkon sabuwar haɗin gwiwa tsakanin jami’a da hukuma ta gargajiya.
Ya nuna cewa ingantaccen haɗin kai zai taimaka sosai wajen magance matsalolin zamantakewa da ci gaba a jihar.
Sarkin ya kuma bayyana cewa Majalisar Sarakuna za ta yi aiki tare da jami’a wajen shirya taruka da bita ga sarakuna, da kuma daidaita rawar da nauyin shugabanci tsakanin masu mukami a fadin jihar Zamfara.
REL/ AMINU DALHATU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
