Kasuwanci
Gwamna AbdulRazaq Ya Yi Jimamin Kisan Jami’in Gandun Daji
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan rasuwar wani jami’in gandun daji, Omotosho Olawuyi Samuel, wanda ya rasa ransa yayin artabu da wasu ’yan bindiga masu garkuwa da mutane a ƙauyen Koro, da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Rafiu Ajakaye, ya fitar, gwamnan ya yaba da jarumtaka da kishin ƙasa da jami’an gandun daji da ’yan sa-kai na tsaro na al’umma suka nuna, inda suka kai farmaki kan ’yan bindigar da ke tserewa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta bayar da tallafin naira miliyan goma (₦10m) ga iyalan mamacin jami’in, a matsayin alamar godiya da jin daɗin gwamnati bisa sadaukarwar rayuwarsa.
Haka zalika, sanarwar ta miƙa ta’aziyya ga iyalan Omotosho Olawuyi Samuel da kuma abokan aikinsa da suka yi yaƙi tare da shi cikin jarumta.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
