Labarai
Shugaba Tinubu Ya Nada Ambasada Isma’il Abba Yusuf Shugaban NAHCON
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON).
Naɗin yana jiran amincewar Majalisar Dattawa, bisa tanadin sashe na 3(2) na Dokar NAHCON ta shekarar 2006.
Shugaba Tinubu ya aike da wasiƙa a yau Laraba 11 ga watan Fabrairun 2026 ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, yana neman a gaggauta tabbatar da naɗin Ambasada Yusuf domin maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan mako bayan kusan watanni 14 yana kan muƙamin.
Ambasada Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne, wanda ya taɓa zama Jakadan Najeriya na Musamman a Jamhuriyar Türkiya daga shekarar 2021 zuwa 2024.
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai19 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
