Labarai
Jigawa: Hukumar Alhazai ta Bai wa Amirul Hajji Tabbacin Cikakken Goyon Baya
Daga Usman Muhammad Zaria
Tawagar Hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar jigawa ta kai ziyarar taya murna ga Amirul Hajji na bana kuma Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Muhammadu Sanusi.
Jagoran tawagar kuma Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bada tabbacin baiwa Amirul Hajjin cikakken hadin kai da goyan baya domin samun nasarar jagorantar aikin hajjin bana.
Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya kuma yiwa Mai Martaba Sarki bayanai game da inda aka kwana game da shirye-shiryen aiki Hajjin bana wanda ya tasamma kaso 40 cikin 100.

Kazalika, ya kuma yi wa Mai martaban bayani akan nasarorin da hukumar ta samu kan batun karbar lamuni daga gwamnatin Jihar domin tare kujerun aikin Hajjin bana.
Ya kuma jaddada cikakken hadin kai da goyan bayansa da na ma’aikatan hukumar ga Amirul Hajji domin sauke nauyi da aka dora masa na jagorantar Alhazan 2026.
A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin kuma Amirul hajjin, ya bayyana jin dadin sa da wannan ziyara.
Ya kuma yabawa hukumar kan tsare tsarenta game da aikin hajjin bana.

Ya na mai nuni da cewar, a matsayinsa na jagora, zai yi aiki tare da hukumar domin samun nasarar gabatar da aikin hajjin bana.
A cewar sa, kamar yadda aka samu nasarar aikin hajjin a 2025,a bana ma za’a samu fiye da bara da izinin Allah.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
