Labarai
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a Ta Gabatar da Kasafin Kuɗi na Naira Biliyan 109 na Shekarar 2026
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a ta gabatar da kimanin naira biliyan ɗari da tara (₦109bn) a matsayin shirin kasafin kuɗinta na shekarar 2026.
Shugaban hukumar, Bashir Abubakar, ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da shirin kasafin gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ɗabi’u, Gatanci da Ƙorafe-ƙorafen Jama’a, wanda Sanata Neda Imasuen, mai wakiltar Edo ta Kudu, ke jagoranta.
Shugaban hukumar ya ce sun gaji PCC ne da matsaloli da dama, musamman waɗanda suka shafi walwalar ma’aikata, ciki har da batutuwan ƙarin girma, tsarin albashi na yanzu, da sauran hakkoki na ma’aikata.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan gabatar da shirin, Bashir Abubakar ya ce manufar kasafin ita ce farfaɗo da ayyukan hukumar domin su gudana cikin tsari mai inganci da tasiri, ta yadda ma’aikata ba za su ci gaba da korafi kan hakkokinsu ba.
Ya ƙara da cewa bai dace ba hukumar da ke kula da ƙorafe-ƙorafen ’yan Nijeriya ta kasance ita ma tana kuka kan take hakkokinta.
Ya tabbatar da cewa, idan aka amince da wannan shiri, za a samu inganta yanayin aiki da walwalar ma’aikata a faɗin ƙasar, wanda hakan zai taimaka wajen cimma nasarori masu ma’ana a aikace-aikacen da doka ta ɗora wa hukumar.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce aikin PCC yana da kamanceceniya da na Kotun Ladabtar da Halayya da, don haka akwai buƙatar a tallafa wa PCC domin ta gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Sanatan ya kuma tabbatar da cewa Majalisar Tarayya na aiki kan gyaran Dokar PCC, da nufin ƙarfafa tsarin doka na hukumar da kuma bunƙasa ƙarfinta na aiwatar da ayyukanta yadda ya dace.
Wannan ci gaba ya yi daidai da ƙoƙarin hukumar na zamani, inganta walwalar ma’aikata, da samun cikakken goyon bayan doka, domin faɗaɗa ƙarfinta wajen karɓa da warware yawaitar ƙorafe-ƙorafen jama’a a Nijeriya.
COV: Bashir Mayere
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
