Labarai
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba ya kaddamar da sabbin shugabannin rikon kwarya na kungiyar ‘yan Achaba na yankin.
A Jawabin da ya gabatar a yayin kaddamarwar a fadar Hakimi, Dr Muhammad Uba yace an nada sabbin shugabanin ne domin samun zaman lafiya a tsakanin su.

Ya kuma hore su da su bi dokoki da ka’idojin kungiya, tare da baiwa Karamar hukumar hadin kai da goyan baya wajen kai rahotan zuwan bakin ‘yan achaba dan tabbatar da tsaro.
Builder Muhammed Uba ya ba su tabbacin samun hadin kai da goyan bayan Karamar hukumar, ya kuma nuna rashin jin dadi da yawan sace sacen babura a yankin.

Kazakika, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kokarin sa na tabbatar da tsaro.
Shi ma a nasa jawabin, Hakimin Birnin Kudu Alhaji Hussaini Hassan jibrin ya bada shawarar yiwa Babura lambobi domin samun saukin ganewa tare da basu horo dan kwarewa akan aikin achaba.

A jawaban su daban daban, Shugaban ‘yan achaba na jihar, Abbas Abdulkadir da sakataren kungiyar, Yau Muhammad sun yabawa shugaban karamar hukumar bisa daukar matakin nada shugabannin riko na kungiyar ‘yan achaba na yankin.
A jawabin sa na godiya, sabon shugaban rikon kungiyar ‘yan Achaba na yankin Auwalu Ibrahim ya bada tabbacin yin aiki bil hakki da gaskiya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
