Connect with us

Labarai

Tinubu Ya Bayyana Alhininsa Bisa Harin Ta’addanci a Kauyen Ngoshe na Jihar Borno

Published

on

Daga Bello Wakili 

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana alhinin sa tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda harin ta’addancin ya shafa a ƙauyen Ngoshe da ke Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Shugaban ƙasar ya yi alhinin rasuwar  mutane da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da jami’an soji, da kuma waɗanda suka rasu sakamakon harbin kuskure yayin da jiragen yaƙi ke kai hari ga ‘yan ta’addan da suka tsere.

Ya bayyana harin na ‘yan ta’addan a matsayin mummunan ta’adi da rashin tausayi ga al’umma marasa ƙarfi, tare da kira ga al’ummar Borno da sauran sassan ƙasar da kada su karaya.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa sojojin bisa  martanin gaggawa da suka mayar, wanda ya yi sanadiyyar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da tilasta musu janyewa daga yankin.

Ya kuma umarci sojoji da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta  ceto mutanen da ‘yan ta’addan suka sace.

Bugu da ƙari, Shugaban ya umarci rundunar sojoji da ta ƙara ƙaimi wajen kare fararen hula a faɗin ƙasar da kuma hana kai hare-hare kan sansanonin soji musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya ji ƙan waɗanda suka rasu a harin da kuma harbin kuskure, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansu da kuma Gwamnatin Jihar Borno.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara