Connect with us

Labarai

Ramadan: Tinubu Ya Kara Jaddada Kudirinsa na Inganta Rayuwar Jami’an Soji

Published

on

Daga Bello Wakili 

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana godiya ga jami’an Rundunar Sojin Najeriya bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare ƙasar, tare da tabbatar musu cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da inganta jin daɗinsu da kuma tallafa wa ayyukansu.

Shugaban ya bayar da wannan tabbaci ne yayin wani taron buɗa-baki na mabiya addinin Musulunci da na Kirista da ya yi tare da jami’an Rundunar Sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya ce taron ya nuna haɗin kan al’ummar Najeriya, yana mai cewa watan Ramadan lokaci ne na yin tunani a kan rayuwa, tsarkake  zuciya da kuma ƙarfafa zaman lafiya tsakanin mabambantan addinai.

Ya yaba wa sojoji kan jajircewarsu wajen kare ƙasa duk da ƙalubalen da suke fuskanta, ciki har da nisantar iyalansu da kuma fuskantar barazanar ‘yan ta’adda da ‘yan Bindiga.

Shugaban ƙasar ya tabbatar musu cewa sadaukarwar da suke yi ba za ta fadi a banza ba, yana mai ƙara cewa jin daɗin sojoji da iyalansu zai ci gaba da kasancewa muhimmin abin da gwamnatinsa za ta bai wa fifiko.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da cewa akwai matsalolin ƙarancin gidaje ga sojoji, yana mai cewa gwamnati na aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki domin magance matsalar.

Dangane da halin tattalin arzikin ƙasar, shugaban ya bayyana cewa duk da cewa Najeriya ta fuskanci ƙalubale masu tsanani a farkon mulkinsa, matakan da gwamnati ta ɗauka sun fara haifar da Da mai ido.

Ya bayyana kwarin gwiwa cewa ƙasar ta fara fita daga mawuyacin hali na tattalin arziki, tare da bada tabbacin cewa nan gaba kadan za a kara ganin canji mai ma’ana a Najeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma miƙa ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Borno kan wani sabon lamari na rashin tsaro da ya faru a jihar, yana mai cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin da ake yi domin kawo ƙarshen ta’addanci da ‘yan bindiga a faɗin ƙasar.

Tun da farko, Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya gode wa shugaban ƙasa bisa shirya taron buɗa-bakin na haɗin gwiwar addinai, tare da yaba masa kan amincewa da matakan da nufinsu shi ne inganta jin daɗin jami’an rundunar soji.

Ya kuma yaba wa shugaban ƙasan kan amincewa da ƙarin albashi ga sojoji, ƙarin alawus ga rundunar Brigade of Guards, da kuma amincewa da sayen sabbin kayan aiki da inganta matsugunan sojoji.

Laftanar Janar Shaibu ya ce waɗannan matakai za su taimaka matuƙa wajen ƙara inganta aikin rundunar da kuma ƙarfafa gwiwar jami’anta.

Haka kuma ya sake jaddada biyayyar rundunar sojin ƙasa ga shugaban ƙasa, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare dimokuraɗiyyar Najeriya da kuma martabar ƙasar.

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai23 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara