Labarai
NSCDC Ta Kama Mutane Biyu Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne a Kwara
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC a Jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da alaka da ’yan bindiga a karamar hukumar Patigi.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ayoola Ishola, ya fitar, ya ce an kama Abubakar Jubril da Mohammed Abubakar ne bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai bisa bayanan sirri.
Sanarwar ta ce an hango mutane uku a wani yanki mai fama da matsalar tsaro, inda aka kama biyu daga cikinsu, yayin da daya ya tsere kuma ake ci gaba da nemansa.
An kuma kwato wasu kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin da suka hada da bindiga karama, wayar salula, da wasu kwayoyi da ake zargin Tramadol ne, da kuma taba sigari.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, kwamandan NSCDC a jihar, Bala Bodinga, ya ce hukumar za ta ci gaba da yaki da ayyukan ta’addanci domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma gargadi masu aikata laifi su daina, tare da bukatar jama’a su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaki da laifuka.
Ali Muhammad Rabi’u/Ilorin
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
