Fasaha
Dalibai Makarantun Sakandare A Kwara Sun Karɓi Tallafin Karatu
Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al’ummomi a kananan hukumomin Edu/Patigi/Moro na jihar Kwara sun samu tallafin karatu don tallafa musu.
Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin karatu da aka gudanar a Ilorin, mai taken “Hatsarori na Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu” wanda Michael Imoudu tare da hadin gwiwar mamba mai wakiltar mazabar Edu/Moro/Patigi na Jihar Kwara, Ahmad Adamu -Saba ya shirya, ya ce za a yi rabon ne kashi biyu.
Dan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa, Muhammed Salihu, ya ce manufar shirin bayar da tallafin shi ne tallafawa daliban da iyayensu ba za su iya biyan wasu kudadensu a makaranta ba.
Saba ya bayyana cewa wasu ’yan gata da ke makaranta suma za su iya amfani da kudin wajen siyan littattafansu ko biyan kudin hayar gidansu .
Ya shawarci daliban da su tabbatar sun yi amfani da naira dubu dari da ake baiwa kowannen su domin manufar da aka sa a gaba.
Saba ta bukace su da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u domin samun ingantacciyar rayuwa.
A nasa jawabin mukaddashin Darakta Janar Michael Imoudu National Institute For Labour Studies (MINILS), Fasto Ezekiel Ayorinde, wanda babban jami’in kula da harkokin kasuwanci na Cibiyar, Hassan Surajudeen ya wakilta, ya ce an raba tallafin ne da nufin inganta ilimin daliban.
Ya kuma shawarce su da su sanya kudin cikin hikima wajen neman ilimi.
A jawabansu daban daban wasu shugabannin al’umma a kananan hukumomin Moro/Edu/Patigi, Muhammed Aliyu Labas da Mohammed Baba (Shonga) sun yabawa mai gudanar da wannan karimcin.
Sun bukaci wadanda suka ci gajiyar kudin da su tabbatar sun yi amfani da kudin don manufar da ake son yi.
A cikin laccar sa mai taken “Hadarin Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi A Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu” Babban Malamin, Abdullahi Galadima ya ce daga bayanan da ake da su matasa na da dabi’ar shiga shaye-shayen miyagun kwayoyi saboda matsin lamba na tsarawa da dai sauransu.
Ya shawarci matasa da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi, su kuma yi karatun ta natsu domin kyautata rayuwarsu
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
