Labarai
Ana Shirin Kaddamar da Sabon Shirin Karatu Kan Cutuka Masu Yaduwa
Cibiyar Kasa ta Lafiyar Jama’a da Cututtuka Masu Yaduwa ta bayyana shirin kaddamar da wani sabon shirin karatu domin kara inganta kwarewar ma’aikatan lafiya wajen yaki da cututtuka masu yaduwa.
Babban Daraktan cibiyar, Dakta Abdullahi Aminu Dalhatu, ya bayyana hakan a wajen rufe taron bitar tsara manhajar karatun National Diploma a fannin cututtuka masu yaduwa da alluran rigakafi, da aka gudanar a Zariya.
Ya ce a baya ana koyar da wannan fanni ne a matakan difloma na gaba da kuma kwasa-kwasan takardar shaida, lamarin da ya bar gibi a matakan ma’aikatan lafiya na tsaka-tsaki.
A cewarsa, sabon shirin zai bai wa dalibai ilimi da kwarewar gano cututtuka, hanyoyin kariya da kuma yadda za a kula da su.
Dakta Dalhatu ya kara da cewa cututtuka masu yaduwa na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar jama’a a Najeriya da sauran kasashe masu zafi.
Shi ma Sakatare na Hukumar Ilimin Fasaha ta Kasa NBTE, Farfesa Idris Muhammad Bugaje, ya ce shirin zai taimaka wajen karfafa horas da kwararrun ma’aikatan lafiya a Najeriya.
Masana da suka halarci bitar sun kuma ba da shawarar a fara aiwatar da shirin a kalla a wata cibiyar kafin karshen shekarar nan.
Ibrahim Suleiman/Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
