Labarai
Cibiyar Ilimin ’Ya’ya Mata Ta Buƙaci Ci Gaba da Goyon Bayan Ilimin ’Yan Mata
Cibiyar Ilimin ’Ya’ya Mata ta yi kira ga iyaye, shugabannin gargajiya da na addini da su ci gaba da bayar da goyon baya wajen inganta ilimin ’yan mata masu tasowa.
Mai Kula da Ayyukan Cibiyar, Malama Alawiya Abdullahi, ta yi wannan kiran ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na kwana guda, da aka gudanar a dakin taro na cibiyar da ke Sabon Gari GRA a Zariya.
Malama Alawiya Abdullahi ta bayyana cewa shirin ya mayar da hankali ne kan bai wa ’yan mata masu shekaru daga goma sha ɗaya zuwa goma sha shida ilimin karatu da lissafi, musamman waɗanda ba sa zuwa makaranta ko kuma suka daina zuwa.
Ta ƙara da cewa taron shi ne karo na huɗu da cibiyar ta shirya domin tantance ci gaban aikin, tattauna ƙalubale da kuma ƙarfafa mallakar shirin daga al’umma.
Saboda haka, mai kula da aikin ta yi kira ga sarakunan gargajiya da limamai da su ƙara wayar da kan al’umma, tare da ƙarfafa iyaye su bai wa ’ya’yansu mata damar samun ingantaccen ilimi.
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da shirin, suna bayyana yadda ya samar da alfanu mai yawa ga al’ummominsu, musamman wajen faɗaɗa damar ilimi ga ’ya’yansu mata.
Maharta taron sun yanke shawarar yin aiki tare domin bunƙasa ilimin ’yan mata da kuma tabbatar da ɗorewar shirin a cikin al’ummominsu.
A yayin taron, mahalarta sun bayar da shawarwari tare da shiga tattaunawar rukuni-rukuni da jami’an shirin suka jagoranta.
Taron ya samu halartar mahalarta daga ƙananan hukumomin Giwa, Makarfi, Sabon Gari da Zariya.
Ibrahim Suleiman/Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
