Ilimi
Makarantar ‘Ya’yan Sojoji Ta Zaria Ta Yi Bukin Cika Shekaru 70 Da Kafawa
Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin cika shekara 71 da aka gudanar a filin faretin RSM Zakari Kumasi dake harabar makarantar a zaria.
Shugaban rundunar mayakan saman ya bayyana cewa makarantar ta NMS ta yi fice wajen baiwa yara horo a fannonin karatu da kuma ilimin aikin soja wanda hakan ya sa ta samar da manyan sojoji da dama har ma da shi a ciki.
Air Marshal Abubakar ya ce bukin na da matukar muhimmanci gare shi,kasancewar sa tsohon dalibin makarantar.
A don haka sai ya yaba wa makarantar ta NMS bisa kasancewar ta akan turbar da aka santa da shi na samar da jajirtattun sojoji ga rundunar mayakan sama ta kasa tsawon shekaru 71 da kafa ta.
Shi ma a nashi jawabin, shugaban kungiyar tsoffin daliban makarantar, Laftana Kwamanda Sunday Ngegu mai ritaya, ya ce kasancewar shugaban rundunar mayakan sama tsohon dalibi a makarantar ya rinka taimaka wa kungiyar, inda ya bukaci sauran tsoffin daliban da suyi koyi da hakan.
Sunday Ngegu ya kuma yaba wa shugaban rundunar mayakan saman bisa gudunmuwar da ya baiwa kungiyar har ta samu nasarorin da ta samu.
Daliban makarantar sun gudanar da faretin ban girma ga manyan baki,yayin da kuma shugaban rundunar mayakan saman ya kaddamar da dakin shan magani na dalibin da babban dakin cin abinci tare da Kwamandan rundunar soji ta daya da sauran Kwamandodin rundunonin soja gami da mai masaukin baki na NMS.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
