Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Ayukka 16 A Sakkwato
A wani babban ci gaba na kawo sauyi a tsarin kiwon lafiyar Najeriya, gwamnatin tarayya ta yi ta kaddamar da ayyuka 16 a asibitin masu tabin hankali na gwamnatin tarayya dake Kware a jihar Sokoto.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Ministan Kasa a ma’aikatar Lafiya da walwalar jama’a, Dokta Iziak Salako, ya jaddada cewa ayyukan na daga cikin ajandar sabuwar fata ta gwamnati shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na kasa.
Ya ce FG ta himmatu wajen samar wa asibitoci kayayyakin more rayuwa, kayan aiki da kudade, da tallafi don inganta ayyukan hidima a fadin kasar.
Dakta Salako ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta samar da muhimman ayyuka sama da 500 na samar da ababen more rayuwa tare da samar da ingantattun kayan aikin jinya ga manyan cibiyoyin kiwon lafiya a fadin kasar nan.
Ministan ya kuma bayyana cewa FG ta dauki ma’aikatan lafiya sama da 15,000 aiki a karkashin shirin bunkasa sana’o’in da ake yi.
Dokta Salako ya ce ma’aikatar lafiya ta fara aiwatar da dokar kula da lafiyar kwakwalwa ta Najeriya, 2023, da nufin samar da cikakken sashen kula da lafiyar kwakwalwa a wani yunkuri na hada ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa cikin harkokin kiwon lafiya na farko a fadin kasar nan.
Rediyon Najeriya da ke Sokoto ya rawaito cewa sabbin ayyukan da aka kaddamar sun hada da dakin gwaje-gwaje na Molecular, Sashen Kula da Lafiyar Jama’a, ICU, Cibiyar Kula da Dogaro da Magungunan Mata da Yara na Yanki, Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa, Dakunan kwanan dalibai da yawa, Makarantar Koyon kula da masu tabin hankali, ICT da dai sauransu.
Shima da yake nasa jawabin, kwamishinan lafiya na jihar Sokoto, Dakta Faruku Wurno, ya nanata kudurin jihar na yin hadin gwiwa da asibitin ta Kware, inda ya bayyana yadda tsarin kula da lafiya na asibitin zai karfafa hadin gwiwa da bayar da hidima.
Dokta Wurno ya yabawa Daraktan kula da lafiya na asibitin Farfesa Shehu Sale bisa jajircewarsa da ya yi, ya kuma bukaci wadanda suka gaje shi da su kara azama kan taswirar ci gaban da aka riga aka shimfida.
NASIR MALALI
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
