Kasuwanci
Zamu Tabbatar da Ingantuwar Depon Sojoji Na Zaria – Ministan Tsaro Badaru

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi alkawarin inganta sansanin horas da kuratan sojoji dake Zaria wato Depot domin baiwa hukumar Soji damar ci gaba da aikin horaswa a wajen.
Ministan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya kai ziyarar tantance sojojin Najeriya da ke Chindit Cantonment a Zariya.
Ministan ya kuma ce, ma’aikatar tsaro ba za ta bar wani abu ba, wajen tabbatar da cewa makarantar firamare ta Chindit ta samu ingantuwar kayan aiki don dacewa da tsarin zamani a matsayin hanyar kara kwarin gwiwa na hafsoshi da sojoji na Kantoment da ke amfana da wajen.
Ya kara da cewa ofishin sa zai hada kai da gwamnatin jihar Kaduna domin ganin an kammala makarantar sakandare ta Chindit.
Ministan ya kuma yi alkawarin taimakawa wajen hakar wasu rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin kara inganta rijiyoyin burtsatse da ke cikin Depot din domin rage kalubalen da ke tattare da samar da ruwan sha a yankin.
Da yake jawabi tun da farko, kwamandan, Depot, Manjo Janar Ahmed Mohammed ya gode wa ministan bisa wannan ziyara, sannan ya kuma sanar da shi yadda babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede ya yi don magance kalubalen da ke fuskantar Depot din.
Ya kuma bayyana fatan cewa wannan hadin gwiwa zai sanya Depot a kan hanyar da ta dace don ganin ta cika aikinta na samarda sojojin Nijeriya.
Kwamandan ya bada tabbacin cewa za a kula da jin dadin ma’aikata da wadanda aka dauka yadda ya kamata domin tabbatar da cewa hukumar ta samu cikakkiyar damar cimma muradun Najeriya.
REL/HALIRU HAMZA
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27