Ilimi
Kwara Ta Gargadi Jama’a Akan Gine-Gine Akan Bututun Ruwa
Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi mazauna jihar kan yin gine-gine a kan bututun ruwa a fadin jihar.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar, Usman Yunusa Lade, ya yi wannan gargadin a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban bututun ruwa dake Flower Garden, a Ilorin.
Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Sakatariyar Dindindin, Misis Christiana Asonibare, ta ce “kamar gine-gine, masallatai, coci-coci da shaguna a kan bututun ruwa da jama’a ke yi yana da illa ga samar da isasshen ruwa a fadin jihar.”
Yunusa -Lade ya yi kira ga daukacin mazauna yankin da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar yin la’akari da bututun ruwa kafin a gina wani gini domin kaucewa lalata bututun ruwa da hana ruwa gudu ga al’umma.
A nasa bangaren babban Injiniya mai kula da aikin gyaran bututun da aka gyara a lambun Flower, Bamidele Idowu, ya tabbatar da cewa an kammala gyaran kuma za a gudanar da gwajin domin tabbatar da cewa ba a samu matsala ba.
Idowu ya bada tabbacin cewa yankunan da suka hada da Flower Garden, Lajorin, Offa Road, Sabo-Oke, Amilengbe, Adualere, Isale-koko, Oja-Gboro, da Ipata da dai sauransu za su ci gajiyar kammala gyaran da zarar an fara aikin turo ruwa.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
